Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana wasu daga cibiyoyin haramtaciyar kasar Isra’ila da za su fuskanci hare-harenta na mayar da martani a nan gaba
Bayan kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, shahidi Isma’il Haniyyah a birnin Tehran da kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah a birnin Beirut, tare da jaddada goyon bayan gwagwarmaya a birnin Falasdinu da Lebanon, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari da makami mai linzami kan haramtacciyar kasar Isra’ila a matsayin mayar da martani, inda suka tarwatsa wasu muhimman wuraren soji guda uku.
Bayan wannan harin da aka kai da makami mai linzami wanda ya kai ga daidai inda aka tsaita shi, jami’an yahudawan sahayoniyya sun yi barazanar mayar da martani da kai wa Iran hari, to sai dai wadannan barazanar sun gamu da gargadi daga manyan jami’an Iran da kwamandojin sojinta.
Jami’ai da shugabannin soji a Iran sun jaddada cewa: Hari na gaba ba zai takaita kan cibiyoyin soji kawai ba, inda zai hada da cibiyoyi masu muhimmanci da suka hada da na rayuwa na yahudawan sahayoniyya.