Sudan ta musanta batun cewa ta mayar da babban birnin kasar na wucin gadi daga Port Sudan zuwa Atbara
Kakakin gwamnatin Sudan, Graham Abdul-Qadir, ya musanta labarin mayar da babban birnin kasar na wucin gadi daga Port Sudan zuwa birnin Atbara, yana mai cewa wannan labarin ba shi da tushe.
Gwamnatin Sudan ta dauki Port Sudan a matsayin hedikwatarta na wucin gadi bayan da Khartoum babban birnin kasar ya koma fagen yaki tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa.
A baya-bayan nan ne dai aka ruwaito cewa: Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Kasar kuma Kwamandan Sojojin Sudan Abdul Fattah Al-Burhan ya yanke shawarar mayar da fadar mulkin kasar daga Port Sudan zuwa birnin Atbara tare da ba da umarnin rarraba ma’aikatun gwamnati zuwa jihohi daban-daban.
Amma mai magana da yawun gwamnatin ya ce; Wannan labarin ba gaskiya ba ne, kuma babu wata shawara ko umarni da hukumomin Sudan suka fitar kan abin ya shafi hakan.
Haka kuma, ya yi nuni da cewa: A baya an rarraba ma’aikatu da dama zuwa jihohin da suka shafi yanayin ayyukansu.