Masu Gwagarmaya A Kasar Iraki Sun Kaddamar Da Sabon Makami Mai Linzami Kan HKI

Dakarun Hashdush- Shaabi na kasar Iraki sun kaddamar da sabbin hare hare da sabbin makamai a kan HKI a dai dai lokacinda ake cika shekara

Dakarun Hashdush- Shaabi na kasar Iraki sun kaddamar da sabbin hare hare da sabbin makamai a kan HKI a dai dai lokacinda ake cika shekara guda da fara yakin Tufanul Aska.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dakarun na Hashdu na fadar haka a shafinsu na Telegram a. Labarin ya kara da cewa sabon makamin da suka gabatar suka kuma yi amfani da shi a wannan karon, shi ne makami mai linzami shamfurin Cruse mai suna Al-Arqab. Kuma sun cilla makamai biyar ne a kan wuraren sojoji na HKI.

Dakarun Hashdu -shaabi dai an samar da su ne a shekara 2014 don yakar kungiyoyin yan ta’adda wadanda suka mamaye kasar Iraki da Siriya a lokacin. Kuma sun sami nasarar wargaza kungiyar ISIS a shekara ta 2017.

Sai kuma bayan fara yakin tufanaul Aksa, gamayyar dakarun kungiyar sun kaddamar da hare hare da dama kan HKI da kuma kan sansanonin sojojin Amurka da suke kasar, don tilastawa sojojin ficewa daga kasarsu. Har’ila sun kai wadan nan hare hare ne don tallafawa mutanen kasashen Falasdinu da kuma Lebanon wadanda sojojin HKI suke zalunta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments