Shugaban Kasar Iran Ya Ce Amurka Da Kasashen Turai Suna Goyon Bayan Hare Haren HKI A Gaza, Sannan Suna Shiru Kan Ta’asar Da HKI Take Aikatawa

Shugaban kasar Iran Masoud Paezeskiyan ya yi allawadai da Amurka da kuma kasashen Turai saboda goyon bayan da suke bawa HKI a kissan kiyashin da

Shugaban kasar Iran Masoud Paezeskiyan ya yi allawadai da Amurka da kuma kasashen Turai saboda goyon bayan da suke bawa HKI a kissan kiyashin da ta yi a Gaza da kuma kasar Falasdinu da aka mamaye da kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IP  na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a yau Talata a nan birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa: Shuwagabannin wadannan kasashen ne suke babatu a kan kasar Iran idan ta zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya yi kissan kai, mu kuma sai mu ce me yasa kuke goyon bayan kissan mata da yara da HKI take yi a kasashen yammacin Asiya?.

A wani bangaren kuma a cikin jawabinsa shugaban ya bayyana muhimmancin hada kan al-ummar musulmi don fuskantar makiyansu. Shugaban ya yi wannan jawabin ne kwana guda da cika shekara guda da fara yakin tufanul Aksa a kasar Falasdinu da aka mamaye, wato a ranar 7 ga watan Octoban  shekarar ta 2023. Inda ya zuwa yanzu sojojin HKI sun kashe falasdinawa fiye da dubu 42. Mafi yawansu mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments