An Gudanar Da Zanga Zanga A Kasashen Duniya Da Dama Don Goyon Bayan Falasdinawa

Dubban mutane a kasashen duniya da dama ne suka fito kan tituna don nuna goyon bayansu ga mutanen kasar Falasdinu da aka mamaye da kuma

Dubban mutane a kasashen duniya da dama ne suka fito kan tituna don nuna goyon bayansu ga mutanen kasar Falasdinu da aka mamaye da kuma mutanen Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-News na kasar Iran ya bayyana cewa dubban daruruwan mutanen a kasashen duniya daban daban ne suka fito zanga zangar yin allawadai da HKI da kuma goyon bayan Falasdinawa da kuma Mutanen kasar Lebanon.

Labarin ya kara da cewa daga cikin kasashen akwai Najeriya, Jamus, Agentina, Amurka, Paru, Pakistan, Jordan da Yemen da sauransu. Masu zanga zangar suna rike da tutocin kasashen Falasdinu da Lebanon, sannan suna rare take ‘yenci ga Falasdinu’ da kuma yin allawadai da HKI. Har’ila yau sun yi kira ga shuwagabannin HKI da su dakatar da kissan kiyashi a wadan nan kasashe da kuma cewa su masu aikata laifin yaki ne.  A jiya Litinin ce ake cika shekara guda da fara yakin tufanul Akasa wanda kungiyar Hamas da kuma sauran kungiyoyin Falasdinawa a Gaza suka kaddamar kan matsugunan yahudawa da suke kewaye da zirin gaza, a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Inda suka kashe wasu sojojin yahudawa a cikin matsugunan sannan suka kama wasu daruruwa suka shiga da su yankin na Gaza. Ya zuwa yanzu dai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa kimani dubu 42, a yayinda wasu dubu 97 kuma suka ji rauni, Sannan wasu fiye da dubu 10 suka bace.

Wannan banda rusa kashi 2/3 na gine gine Gaza. Sun hana shigo da abinci da magunguna da sannan mafi yawan wadanda suka kashe yara da mata ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments