Maduro ya ce ‘Isra’ila’ ta kaddamar da ‘yakin halaka’ a yammacin Asiya

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya jaddada a ranar Litinin din nan cewa, ana ci gaba da yakin kisan kare dangi kan al’ummar Larabawa na

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya jaddada a ranar Litinin din nan cewa, ana ci gaba da yakin kisan kare dangi kan al’ummar Larabawa na Falasdinu, Siriya, wanda kafafen yada labaran yammacin duniya ke boyewa.

A cikin shirinsa na Con Maduro +, shugaba Nicolas Maduro ya bayyana cewa gwagwarmayar da ake yi a halin yanzu ta samo asali ne tun daga yaki da daga muradun ‘yan mulkin mallaka na Amurka, Birtaniya, da Turai, da nufin sarrafa kasashe masu ‘yanci da kuma fadada ikonsu a kan yankin baki daya.

A wani yanayi na tarihi, shugaban ya bayyana cewa Falasdinu ta kasance cibiyar al’adu, addini, yahudawa, da musulmi da kirista,  da zaman tare tsakaninsu  har sai da yan  mulkin mallaka na Amurka, Birtaniya da Turai suka saka kafarsu a yankin ne aka fara rikici.

Ya ci gaba da bayyana cewa bala’in da al’ummar Palasdinu ke fuskanta ya faro ne tun shekaru 76 da suka gabata.

Ya jaddada cewa lamarin ya rikide zuwa wani gagarumin yaki na sahyuniyawa a kan ‘yan asalin kasar Falastinu.

“Yau shekara guda ke nan ana  kisan kiyashi, na yi mamakin cewa akwai kafafen yada labarai, masu taken: Shekara guda na yakin Isra’ila da Hamas. Wannan ba adalci ba ne, Hamas kungiyar kare kasa ce, Isr’ila kuma masu mamaya ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments