Hizbullah ta yi luguden wuta kan wasu wurare na sojin Isra’ila

Kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa mayakanta sun kai wasu jerin hare-haren rokoki kan wasu wuraren da sojojin Isra’ila suka yi dandazo. Dakarun sun kai

Kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa mayakanta sun kai wasu jerin hare-haren rokoki kan wasu wuraren da sojojin Isra’ila suka yi dandazo.

Dakarun sun kai hari kan Nimra daya daga cikin manyan sansanonin sojin Isra’ila a yankin arewa maso yammacin tafkin Tabarayya tare da harba rokoki.

Bayan haka, sun kai hari kan taron motocin sojojin Isra’ila da ma’aikatansu  yankin Jal al-Alam, inda suka kai hari da wani makami mai linzami., yan sa’oi bayan haka kuma sun kai wamni harin a yankin Karmiel.

Hizbullah ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a duk tsawon yini, inda aka kai harin roka kan matsugunan Kfar Vradim, sannan kuma ta kai wani gagarumin farmaki kan wasu gine-gine da ke arewacin Haifa da wani babban  makamin roka.

Da yammacin jiya ne dakarun Hizbullah suka harba makami mai linzami kan wani taron sojojin Isra’ila a tsaunin Qalaat da ke Blida. Hakan ya biyo bayan wani farmaki da aka kaiwa sojojin Isra’ila a Beit Hillel.

A wani mataki na karshe na wannan rana, kungiyar Hizbullah ta harba makamin roka zuwa sansanin na bataliya ta 8200’s Glilot da ke wajen birnin Tel Aviv, tare da jaddada cewa, hakan na da nasaba da kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Lebanon da Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments