Jihar Sokoto Za Ta Gina Sabbin Madatsun Ruwa Uku

Leadership–Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da shirinta na gina dam-dam guda uku tare da sayen traktoci 244 a wani yunƙuri na haɗa kai wajen bunƙasa

Jihar Sokoto Za Ta Gina Sabbin Madatsun Ruwa Uku

LeadershipGwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da shirinta na gina dam-dam guda uku tare da sayen traktoci 244 a wani yunƙuri na haɗa kai wajen bunƙasa aikin Fadama da noman rani.

Dr. Bashir Achida, mai ba da shawara kan tattalin arziki ga Gwamnan Jihar Sokoto, ya bayyana wannan shiri yayin wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.

Sokoto na ɗaya daga cikin manyan yankunan da ke samar da albasa da tafarnuwa a Yammacin Afrika, kuma gwamnati na shirin faɗaɗa hakan domin biyan buƙatar da ke ƙaruwa a nahiyar. Baya ga habaka noma, gwamnatin jihar tana aiki tare da Ma’aikatar Bunƙasa Ma’adanai ta Tarayya don samun lasisin rami-rami da ke ƙunshe da duwatsun ƙasa, da ƙarfe, da zinariya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments