Al-Nakhalah: Hadin kai tsakanin ‘yan gwagwarmaya ya yi tasiri a shekara 1 bayan Guguwar Aqsa

Babban sakataren kungiyar Jihadul  Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya bayyana a cikin jawabinsa na cika shekara ta farko da  fara kaddamar da hare-haren guguwar

Babban sakataren kungiyar Jihadul  Islami ta Falasdinu, Ziyad al-Nakhalah, ya bayyana a cikin jawabinsa na cika shekara ta farko da  fara kaddamar da hare-haren guguwar Aqsa cewa, hadin kan al’ummar Palasdinu na daya daga cikin muhimman lamurra da suka yi tasiri wajen tunkarar mamayar Isra’ila.

A cikin jawabin nasa, al-Nakhalah ya jaddada cewa “haɗin kan dakarun ‘yan gwagwarmaya a yankin yana da mahimmanci don samun nasara.”

Ya kara da cewa, dakarun al-Quds brigades, reshen soji na Jihadul Islami, sun kafa sansanoni a dukkanin fagagen yaki a yankin zirin Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan, inda ya kara da cewa mayakan mu suna fada kafada da kafada da mayakan Qassam na Hamas.

Al-Nakhalah ya tabbatar da cewa manufar kungiyar Jihadul Islami a bayyane take na hadin kan dakarun gwagwarmaya tun bayan kaddamar da farmakin guguwar Aqsa.

A cikin wannan yanayi, babban magatakardar  na Jihadul Islami ya bayyana cewa, “Mun ba wa ‘yan’uwanmu na kungiyar Hamas izinin jagorantar lamarin a fagen siyasa,” yana mai jaddada cewa “Hadin kan al’ummar Palastinu na daya daga cikin muhimman lamurra da suka yi tasiri wajen tunkarar makiya.”

A cikin jawabin nasa, al-Nakhalah ya sake nanata kudurin kungiyar Jihadul Islami kan bukatun da aka sanar a farkon yakin yana mai cewa: “Janyewar sojojin gaba daya daga zirin Gaza, da sake gina yankin, da yarjejeniyar musayar fursunoni.

Ya kuma jinjinawa al’ummar kasar Labanon, da tsayin dakansu, da ruhin babban jagoransu shahid Sayyed Hassan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments