Munafuncin Amurka: Maganar zaman lafiya a kafofin watsa labarai isar da bam a bakin teku

Shugaban Amurka Joe Biden a yayin da yake jawabi a gaban yahudawan sahayoniya a baya-bayan ya bayyana cewa , babu wata gwamnati da ta taimaki

Shugaban Amurka Joe Biden a yayin da yake jawabi a gaban yahudawan sahayoniya a baya-bayan ya bayyana cewa , babu wata gwamnati da ta taimaki Isra’ila fiye da gwamnatina.

A rahoton Pars Today, Biden ya amince cewa shi ne babban mai goyon bayan gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Biden ya kara da cewa, abin da ya dame shi shi ne, yadda zai hana duk wani yaki da zai barke a yammacin Asiya.

Da’awar da Amurkawa ke yi na samar da zaman lafiya da hana tayar da zaune tsaye a yammacin Asiya ya yi hannun riga a aikace da irin da goyon bayan da take baiwa gwamnatin sahyoniyawan danniya.

Amurka da ke fuskantar matsin lamba daga ra’ayin jama’a na cikin gida da na duniya, ta yi ikirarin yin kokarin tsagaita bude wuta da kuma cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin da ke yaki a Gaza da Lebanon.

Wannan ikirari ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Amurka kamar yadda ta saba tana nuna salon siyasarta na harshen damo, kamar yadda hakan ke faruwa a yanzu a gabas ta tsakiya.

Irin Wannan mataki na Amurka ya kara karrfafa gwiwar Isra’ila wajen ci gaba da aikata laifukan yaki a gaza da kuma Lebanon.

A lokacin mulkin Obama, bisa yarjejeniya tsakanin Tel Aviv da Washington, Amurka zata rika bayar da taimako na kayan soji da ya kai na dala biliyan 3.8 ga gwamnatin sahyoniya. Haka kuma, tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, Amma kuma Amurka ta zartar da wata doka wacce ta ba da damar mikawa Isra’ila tallafi a bangaren soji da ya kai na dala biliyan 12.5 ciki har da dala biliyan 3.8 na lissafin watan Maris na 2024, da kuma Karin  dala biliyan 8.7 a cikin Afrilu 2024.

A cewar wannan rahoto, bisa la’akari da tashi sad a saukar darajar dala a shekarar 2022, adadin taimakon da Amurka ke baiwa Isra’ila ya ninka tun tun daga shekarar 1946 zuwa wannan shekara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments