A wata hira da ya yi da mujallar Le Point a cikin kwanakin nan, ministan tsaron Faransa Sebastien Lecornu ya jaddada cewa, a halin yanzu Rasha ita ce babbar abokiyar hamayyar Faransa. Wannan tattaunawa ta zo daidai da fitar da sabon littafin Lecornu, inda ya bayyana kalubalen tsaro da Faransa ke fuskanta a yau.
Lokacin da aka tambaye shi game da babbar barazana ga Faransa, ban da kungiyoyin ta’addanci, Lecornu ya ce, “A bayyane yake cewa Tarayyar Rasha ce.” Ya kara da cewa Moscow ta zama “mafi hadari” a wannan shekara idan aka kwatanta da 2022 da 2023.
Lecornu ya yi ikirarin cewa, Rasha ba tana barazana ba kawai ga muradun Faransa a Afirka ba, har ma tana a matsayin hadari kai tsaye ga Sojojin Faransa da ke wajen kasar.
Bugu da kari, Lecornu ya zargi Rasha da yakin kafofin sadarwa da kuma saba yarjejeniyar makamai masu linzami.
Babban hafsan tsaron Faransa bai fayyace abubuwan da suka faru ba, amma duka kasashen Rasha da NATO na zargin juna da yin safarar makamai masu hadari.
A watan Maris ne Rasha ta yi ikirarin cewa jiragenta sun yi wa jiragen yakin Faransa Rafale rakiya a kan tekun Black Sea. Bugu da kari kuma, Rasha ta yi gargadin cewa makaman da Faransa ke samarwa ga Ukraine na iya haifar da yanayi mai hadari.
Bugu da kari, a cikin watan Janairu, Rasha ta gayyaci jakadan Faransa kan kasancewar ” sojojin haya na Faransa” a Ukraine, wanda Faransa ta amince amma ta musanta hakan.