Bello Turji, ya gindaya sharuɗdan kawo karshen harare da yake jagoranta

https://hausa.premiumtimesng.com. Shahararren ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen satar mutane da karɓar kuɗin fansa, Bello Turji, ya zargi gwamnan Zamfara Dauda Lawal

https://hausa.premiumtimesng.com.

Shahararren ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen satar mutane da karɓar kuɗin fansa, Bello Turji, ya zargi gwamnan Zamfara Dauda Lawal da tsohon gwamnan jihar kuma ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matwalle da siyasantar da batun tsaro a jihar.

Turji wanda ake zargin ya yi ƙaura daga jihar Zamfara tun bayan tsananta hare-hare da rundunar sojin Najeriya ke yi, ya gindaya sharuɗa da za a bi wajen samar da zaman lafiya a jihar.

Ya ce za a samu zaman lafiya a jihar ne idan jami’an tsaro da ‘yan bijilanti suka daina kashe Fulani a jihar da ma sauran johohi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments