MDD : Haramcin Shiga Isra’ila Ga Sakatare-Janar ‘’Kai Hari’’ Ne Kan Ma’aikatanmu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce haramcin tafiye-tafiyen da Isra’ila ta yi kan sakatare-janar ‘kai hari’ ne na baya-bayan nan kan ma’aikatanta. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce haramcin tafiye-tafiyen da Isra’ila ta yi kan sakatare-janar ‘kai hari’ ne na baya-bayan nan kan ma’aikatanta.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce haramcin tafiye-tafiyen da Isra’ila ta yi wa Sakatare-Janar Antonio Guterres “bayani ne na siyasa” kuma hari ne na baya-bayan nan da gwamnatin Isra’ila ta kai wa kungiyar ta duniya.

M. Dujarric ya ce ayyana Guterres da ministan harkokin wajen Isra’ila Katz ya yi a matsayin “wanda ba’a maraba da shi” a Isra’ila “wani hari ne da aka kaiwa ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya.

Ministan harkokin wajen na Isra’ila, ya ce Isra’ila “ba ta maraba” da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres kuma an haramta masa shiga kasar.

Katz ya ce an cimma wannan matsaya ne bisa la’akari da gazawar Antonio Guterres ta kin yin kakkausan suka ga harin da Iran ta kai wa Isra’ilar ranar Talata.

Ya kuma zargi shugaban na Majalisar Dinkin Duniya da “nuna kiyayya ga Isra’ila” da “goyon bayan ta’addanci da fyade da kisan jama’a.

“Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya ba zai taɓa manta wa Guterres ba a matsayin gurbatacce .”

A jiya ne dai sakatare janar na Majalisar Dinkin ta Duniya ya yi tir da abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya inda kuma ya yi kira da a cimma tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments