Sheikh Qassem: Hizbullah ta shirya domin yaki na dogon lokaci da Isra’ila

A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a wannan Litinin , mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya mika sakon

A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a wannan Litinin , mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummar kasar Labanon da sauran al’ummar musulmi da na larabawa kan shahadar Sayyed Hassan Nasrallah, yana mai cewa: “Ina yi muku jawabi a cikin yanayi mafi zafi da bakin ciki a cikin lokutan rayuwata, mun rasa dan uwa, masoyi aboki kuma a matsayin uba, Sayyed Hassan Nasrallah.”

Ya jaddada muhimman batutuwa da dama a cikin jawabin nasa, inda ya jaddada irin jajircewar da kungiyar ta Hizbullah take ci gaba da yi a kan aikinta, wanda ya hada da tinkarar mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila, da kuma ci gaba da goyon bayan Gaza, tare da kare kasar Labanon da al’ummarta.

Sheikh Qassem ya jaddada cewa, duk da hare-hare da kashe-kashen da Isra’ila ke ci gaba da yi, ‘yan gwagwarmaya na ci gaba da yin tsayin daka a fagen daga.

A cikin jawabin nasa mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya sanar da cewa, kungiyar za ta nada sabon Sakatare-Janar cikin gaggawa kamar yadda tsarin da aka kafa ya tanada, yana mai jaddada cewa “zabin yana da sauki,  domin mun hada kai bisa manufa.”

Ya bayyana cewa “a cikin tsarin kungiyar Hizbullah, akwai tsari wanda ya yi tanadin wasu matakai domin ayyana shugaba , ko kuma karbar wani mukami a cikin kungiyar.

Sheikh Qassem ya jaddada cewa, duk da asarar shugabanni da dama, da kuma hare-haren makiya  kan fararen hula, da kuma sadaukarwar da ake yi, “ba za mu yi kasa a gwiwa ba daga matsayinmu.

A cikin wannan mahallin, Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, “Mun san cewa yakin zai dade, kuma a shirye muke mu fuskanci duk wane irin yanayi, domin kuwa mun zamu yi nasara a wannan yaki da yardar Allah.”

Ya kara da cewa, kungiyar Hizbullah a shirye take ta fuskanci duk wani abu da zai iya faruwa idan Isra’ila ta yanke shawarar shiga cikin kasar Lebanon ta kasa. Sheikh Qassem ya ci gaba da cewa, “Muna da shiri sosai kuma muna da tabbaci a kan cewa makiya wato yahudawan Haramtacciyar Kasar  Isra’ila ba za su cimma manufofinsu ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments