Babban Sakataren MDD: Dole ne a kawo karshen rikicin Lebanon kuma a tsagaita wuta a Gaza

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matukar damuwarsa game da halin tashe-tashen hankula a Labanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yana mai

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana matukar damuwarsa game da halin tashe-tashen hankula a Labanon cikin sa’o’i 24 da suka gabata, yana mai yin kira da a kawo karshen wannan tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

“Dole ne a daina wannan tashe-tashen hankula a yanzu, kuma dole ne dukkan bangarorin su amince da hanyoyi na zaman lafiya,” in ji Antonio Guterres a cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar a wannan Litinin.

Guterres ya yi gargadin cewa “yakin gama-gari” zai haifar da mummunan sakamako ba ga kasar Labanon da “Isra’ila” kadai ba, har ma da daukacin yankin gabas ta tsakiya.

Babban sakataren ya bukaci dukkanin bangarorin da su aiwatar da kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1701, wanda ya bukaci a daina yaki.

Ya kuma sake nanata “kiransa na a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza da kuma sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.”

Kalaman nasa, wadanda bai ambaci wanda ya aikata laifin ba, na zuwa ne a daidai lokacin da “Isra’ila” ke ci gaba da kai hare-hare kan al’ummomin Lebanon da zirin Gaza.

A farkon makon da ya gabata ne dai babban sakataren na MDD ya sake yin wani jawabi makamancin haka, inda ya yi kira da a dakatar da wuce gona da iri kan kasar Labanon, yana mai jaddada cewa, duniya ba za ta iya barin Lebanon ta zama wata Gaza ba, yana mai jaddada cewa, “dole ne ko ta wane hali, a kaucewa faruwar yakin  da ba a san karshensa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments