Iran Ta La’anci Harin Isra’ila A Yemen

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren da Isra’ila ta kai kan tashar samar da

Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan hare-haren da Isra’ila ta kai kan tashar samar da wutar lantarki da rijiyoyin mai na kasar Yemen.

“Matakin da gwamnatin Sahayoniya ta dauka na kai hari kan kasar Yemen, wani karan tsaye ne kuma saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya,” in ji Naser Kan’ani a wata sanarwa.

Ya yaba da irin goyon bayan da kasar Yeman ta bayar ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, wadanda Isra’ila ke yi wa kisan kare dangi tun watan Oktoban bara.

Kakakin ya kara da cewa al’ummar kasa da kasa na da wani nauyi da ya rataya a wuyansu na tsayawa tsayin daka domin takawa Isra’ila birki kan yadda ta ke bijirewa dokokin kasa da kasa.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar a jiya Lahadi ta ce jiragen yakinta sun kaddamar da farmaki kan tashar jiragen ruwa ta Ras Isa da ke lardin Hudaidah a yammacin kasar Yemen, inda suka kai farmaki kan cibiyoyin wutar lantarki na al-Hali da al-Khateb da kuma wasu wurare masu mahimmanci dake da alaka da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen.

Kan’ani ya ce irin wadannan munanan hare-hare, wadanda suka lalata kayayyakin more rayuwa na fararen hula a Hudaydah, sun fallasa irin “rashin imani” na gwamnatin Isra’ila.

Ya kara da cewa Isra’ila tana aiwatar da ayyukanta na aikata laifuka tare da goyon bayan Amurka “.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments