Sharhi : Shahadar Sayyid Hassan Nasarallah

A ranar Jumma’an da ta gabata ce jiragen yakin HKI suka kai hare-hare mafi muni a wannan shekara kan unguwar Dhahiya Junubiyya, ta birnin Beirut

A ranar Jumma’an da ta gabata ce jiragen yakin HKI suka kai hare-hare mafi muni a wannan shekara kan unguwar Dhahiya Junubiyya, ta birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon, inda suka kashe Sayyid Hassan Nasarallah babban sakataren kungiyar Hizbullah wace ta dauki shekara guda tana fafatawa da sojojinsu a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye bayan fara yakin Tufanul Aksa.

An kafa kungiyar Hizbullah ne a shekara 1982 wato fiye da shekaru 40 suka gabata, kuma tun lokacinkafata ya zuwa yanzu ta sami nasarori a fagage da dama a cikin kasar Lebanon, da ma kasashen yankin Asia ta kudu. Kuma wasu daga kasashenduniya da dama sun amfana da ita.

Mafi muhimmanci daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu a karshen shugabancin Sayyid Hassan Nasarallah shi ne.

Na farko ta sami nasarar korar sojojin HKI daga kasar Lebanon bayan mamayar da suka yiwa kasar tun shekara 1982. Hizbullah ta sami nasarar korar sojojin yahudawan HKI daga kasar Lebanon a shekara ta 2000, wato bayana mamayar kasar na tsawon shekaru kimani 18.

Banda haka kungiyar tana daga cikin kungiyoyin da suke tallafawa al-ummar Falasdinu wacce kasashen yamma suka kafa kasar HKI a kan kasarsu. Yahudawan sun kashe, sun kora sun kuma azbatar da Falasdinawa sun koresu daga  gidajensu sun kuma daure wasunsu a gidajen yari na shekaru masu yawa ko kuma na tsawon rayuwarsu. Wannan yana faruwa da Falasdinawa kimani shekaru 76 da suka gabata. 

Sai kuma a shekarata 2006 gwamnatin  HKI tare da hadin kai da kasashen yamma musamman Amurka sun yanke shawarar shafe kungiyar Hizbullah daga doron kasa da kuma sake mamayar kasar Lebanon, saboda kashe sojojin yauhawa uku da kuma kama wasu biyu wanda mayakan kungiyar suka yi. Da wanda dalilin suka farwa kasar Lebanon da yake wanda ake kiran yakin watan Yuli, saboda an fara yakin ne a ranar 12 ga watan Yuli sannan aka  tsagaita wuta a ranar 14 ga watan Augusta na shekara ta 2006.

A wannan yakin dakarun kungiyar Hizbullah sun sami nasarar kare kasar Lebanon daga sake mamayarta da HKI da kawayenta suke son yi.

Kuma sun sami nasarar wargaza takokin yakin HKI wadanda suke alfahari da su, da kuma halaka sojojin su masu yawa, wannan hakan ya tilastawa HKI amincewa da dakatar da budewa juna wuta da dakarun kungiyar.

Sai kuma a shekara ta 2011 kasashen yamma sun samar da kungiyar yanta’adda ta Daesh ko ISIS wadanda suka mamaye kasashen Iraki da Siriya. Suka kuma kwace iko da wasu yankuna a cikin wadannan kasashe. Manufarsu turawan itace yayyaka kasashen biyu zuwa kananan kasashe wadanda ba za su iya fada da HKI ba.

Kuma da haka zasu raba kungiyar Hizbullah da JMI, sannan a hankali su sake dawowa kasar Lebanon su murkushe kungiyar Hizbullah.

A nan ma kungiyar Hizbullah tare da hadin kai da gwamnatocin  kasashen Syriya da Iraki da kuma rundunar Qudus ta JMI. Har’ila yau da kuma dakarun Hashdushaabi da aka kafa a kasar Iraki bayan mamayar Daesh, karkashin jagorancin Janar Kasim Sulaimani suka kawo kashe kungiyar Deash a kasar Iraki da mafi yawan kasar siriya a shekara ta 2017.

Banda haka kungiyar Hizbullah ta fatattaki yan ta’adda wadanda Amurka da kawayenta na kasashen larabawa suka samar, wadanda kuma suka mamaye wasu yankuna na kasar Lebanon. Da haka kuma suka bata Shirin Amurka da kasashen yamma da wasu kawayensu na kasashen Larabawa a kasashen Iraki da Siriya.

A halin yanzu Amurka tare da kasar Turkiyya suna mamaye da wani yanki a gabacin kasar Siriya. Sun kuma bawa wasu yan ta’addan mafaka, har suka shimfida gwamnatinsu a lardunan Hasaka da Idlib a areaway maso gabacin kasar Siriya. Haka kuma sun bawa kurdawan kasar Siriya damar iko da wasu yankunansu a kasar. A shirinsu na rarraba kasar.

Banda haka sojojin Amurka da sunan yaki da kungiyar Daesh wacce suka kafa da kansu, sun kafa wata kawance ta yaki da Daesh ko ISIS, bayan da Hizbullah da kawayenta suka sami nasarar kawo karshen kungiyoyinsu na ta’adda a wadannan kasashe biyu, sojojin Amurka sun ci gaba da kasancewa a kasashen siriya da Iraki sun kafa sansanoninsu a lardin Hasaka na kasar Siriya da kuma wani wuri a kan iyakokin kasashen Siriya, Jordan da kuma Iraki, mai yuwa saboda shirya wani makirci wa kasashen larabawan ko kuma don kare HKI daga duk wani hatsarin da zai zo mata.

Sannan bayan fara yakin Tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, kungiyar Hizbullah ta shiga yaki da HKI don tallafawa falasdinawa a Gaza, kuma ya zuwa shekara kimani guda da ta gabata ta sami nasarar korar yahudawan kimani dubu 80,000 daga arerwacin kasar Falasdinu da aka mamaye.

Don haka duk tare da kissan kiyashin da sojojin HKI suka yi a gaza, da kuma rusa kimani kashi 2/3 na gine gine Gaza, yahudawan sun kasa murkushe Falasdinawa a Gaza, ga kuma yahudawan da aka kora.

Don haka muhimmancin kungiyar Hizbullah ga kasar Lebanon ga kuma kasashen  yankin Asia ta kudu ba a boye suke. Kuma dukkan wadannan nasarorin wadanda kungiyar ta samu a cikin gida ko kuma yankin, sun faru ne tare da shugabancin Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.

Da wannan dalilan ne da wasu da dama ya sa HKI ta yanke shawarar kashe shi. Mai yuwa a zatonsu zata kawo karshen kungiyar Hizbulla sannan su yi abinda suka ga dama.

Daga karshe yakin tufanul Aksa da kuma kashe falasdinawa fiye da 40,000 a gaza, da kuma kisan shuwagabannin kungiyoyu masu gwagwarmaya a yankin, wadanda suka hada da sayyid Hassan Nasarallah, da Isma’il Haniyyar shugaban kungiyar Hamas da wasu kwamandoji da jagororin Hizbullah da Hamas, duk wadannan sun fallasa kasashen yamma musamman Amurka wadanda suke goyon bayan HKI a dukkan wadannan ayyukan ta’adancin da tayi kuma take ci gaba da yi a yankin.

A cikin shekara guda da ta gabata, Amurka ta hana kudurorin MDD ta tsagaita wuta a gaza har sau hudu tsallawa a kwamitin tsaro na majalisar. sannan itace a gaba gaba wajen bawa HKI makamai a fili da boye. Sannan ta hana a aiwatar da hukuncin kotun kasa da aka na kama Natanyahu da hukunta shi kan kisannan falasdinawa fiye da dubu 40 mafi yanwasu mata da yara a Gaza.

Har’ila yau a cikin shekara guda da ta gabata ne, mutuncin MDD ta fada, don ta zama bata da amfani wajen kare Falasdinawa da kuma kare hakkin bil’adama, Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da dama, da na bada agaji duk sun tashi daga aiki, saboda abinda zasu iya yi kawai a yakin gaza shi ne allawadai da HKI.

Don Haka masana suna ganin kashe Sayyid Hassan Nasarallah zai yi tasiri ko ya zai sauya al-amura da dama a kasar Lebanon, kasashen yankin Asia ta kudu da kuma sauran kasashen duniya.

Masu sauraro karshen sharhin bayan labaran kenan.

===============

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments