Gwamnatin Amurka Ta Bada Sanarwan Cewa HKI Ta Fara Shiga Kasar Lebanon Ta Kasa A Hankali

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wani jami’in gwamnatin kasar Amurka yana fadawa tashar talabijin ta ABC. Jami’an ya kara da cewa

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wani jami’in gwamnatin kasar Amurka yana fadawa tashar talabijin ta ABC.

Jami’an ya kara da cewa sojojin  HKI sun fara Shirin mamayar kasar Lebanon nan gaba kadan, saboda suna ganin kashe shuwagabannin kungiyar Hizbullah kadai bai wadatar wajen samar da aminci isa ba. Dole ne sai sojojin HKI sun kwace wasu yankuna a kasar ta Lebanon don tabbatar da amincin arewacin HKI kafin ta fara maganar komawar yahudawan da suke arewacin kasar.

Jami’in ya ce dole ne gwamnatin HKI ta wargaza dukkan makamai na kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon. Idan ba haka tayi ba to kuwa ba zata samu zaman lafiya mai dorewa a kasar ba.  

Daga karshen Jami’in ya bayyana  cewa kissan da sojojin HKI suka yiwa Sayyid Hassan Nasarallah shugaban kungiyar Hizbullah ya hargitsa al-amura da dama a yankin gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments