Jami’i Mai Kula Da Al-Amuran Harkokin Waje Na Tarayyar Turai (EU) Ya Ce Babu Wanda Zai Dakatar Da Natanyahu Kan Abinda Yasa A Gaba

Jami’i mai kula da al-amuran kasashen waje na tarayyar Turai Josep Borrell ya bayyana cewa yana ganin a duniyan nan ba wanda ya isa ya

Jami’i mai kula da al-amuran kasashen waje na tarayyar Turai Josep Borrell ya bayyana cewa yana ganin a duniyan nan ba wanda ya isa ya dakatar da Natanyahu firai ministan HKI ko da kuwa gwamnatin Amurka ce.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Borrel yana fadar haka a jiya Jumma’a, a gefen taron babban zauren MDD a birnin New York na kasar Amurka. Ya ce Natanyahu ya sha alwashin murkushe kungiyoyin Hizbullah da kuma Hamas. Kuma da alamun ba wanda zai hana shiyin hakan.

Borell ya ce yana goyon bayan shawarar kasar Faransa ta bayar na tsagaita wuta mai tsawon makonni 3 amma gwamnatin HKI ta ki hakan.  Daga karshe Borell ya kammala da cewa da alamun zamu shiga yaki mai tsawo a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments