Hizbullah Tana Cigaba Da Kai Wa HKI Hare-Haren Mayar Na Martani

A jiya Alhamis mayakan kungiyar ta Hizbullah sun sanar da harba makamai masu linzami a sassa daban-daban na HKI da su ka hada da kamfanin

A jiya Alhamis mayakan kungiyar ta Hizbullah sun sanar da harba makamai masu linzami a sassa daban-daban na HKI da su ka hada da kamfanin kera makamai na “Rufael a arewacin Haida. Har ila yau dakarun na Hizbullah sun kai wani harin da makamai masu linzami akan sansanin soja na “Daud” da can ne cibiyar rundunar sojan ‘yan mamaya dake Arewa, sai kuma wuraren ajiye makamai na “Ami’ad.

Wani sansanin da dakarun Hizbullah su ka kai wa hari da jiragen sama marasa matuki,shi ne na Shamshun tare da yin barna a cikinsa.

A cikin Lebanon mayakan Hizbullah sun yi amfani da wasu makamai akan jiragen yakin ‘yan mamaya da hakan ya tilasta musu komawa inda su ka fito.

A jiya Alhamis kadai,dakarun Hizbullah sun harba makamai masu linzami fiye da 80 akan garin Safad, haka nan kuma sansanin ‘yan share wuri zauna na Kiryat-Ata.

Da safiyar yau Juma’a ma dai Hizbullah ta harba makamai masu linzami a sassa daban-daban na HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments