Houthi : Yemen ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafawa Lebanon

Shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-Malik al-Houthi ya ce kungiyar gwagwarmayar Yeman ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafa wa Labanon da Hizbullah kan

Shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-Malik al-Houthi ya ce kungiyar gwagwarmayar Yeman ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafa wa Labanon da Hizbullah kan yiwuwar mamaye kasar daga makiya na Isra’ila.

A wani jawabi ta gidan talbijin yau Alhamis, Al-Houthi ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanonmai manufar hana Hizbullah “goyon bayan Gaza da al’ummar Falasdinu”.

Ya ce, kara kai hare-hare da Isra’ila ke yi kan kasar Labanon, “tsarin wuce gona da iri ne” wanda aka shafe shekaru da dama ana yi, yayin da yake tabbatar da cewa kungiyar Hizbullah ta fi karfi fiye da kowane lokaci.

“Makiya yahudawan sahyoniya suna kokarin yin amfani da hanyar aikata laifuka iri daya a Gaza a kasar Lebanon, da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, da kashe fararen hula da lalata gidajensu.

Al-Houthi ya ce nasarori da kungiyar Hizbullah ta samu ya nuna muhimmiyar rawar da kungiyar gwagwarmaya ke takawa a kasashen Lebanon da Falastinu da daukacin al’ummar musulmi.

“hakan ya dace da muradun Lebanon, domin idan makiya suka cimma burinsu a Falastinu, to tabbas Lebanon za ta fuskanci hare-haren yahudawan sahyoniya, inji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments