Mali, Burkina da Nijar Na Binciken Dan Jaridar France24 Kan Ta’addanci

Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun kaddamar da bincike kan wani wani dan jarida na tashar talabijin ta France24, mai suna Wassim Nasr, kan

Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun kaddamar da bincike kan wani wani dan jarida na tashar talabijin ta France24, mai suna Wassim Nasr, kan zargin goyan bayan ta’addanci”.

Masu gabatar da kara daga kasashen uku da ke karkashin mulkin soji sun kaddamar da bincike kan Wassim Nasr, saboda wani bincike da ya gudanar game da ayyukan ‘yan ta’adda masu ikirari da sunan jihadi.

A baya baya nan Nasr, ya fitar da wani rahoto game da hare-haren wasu ‘yan ta’adda a yankuna masu muhimmanci a Bamako, babban birnin Mali a ranar 17 ga Satumba.

Masu gabatar da kara daga sashen shari’a da suka kware kan yaki da ta’addanci a Mali, Burkina Faso da Nijar sun fitar da sanarwa iri guda, wadda aka sanar a kafafen yada labaran kasashen a yammacin ranar Laraba, inda suka zargi Nasr da yin sharhi da “zama mai nuna goyon baya da yada manufofin ‘yan ta’adda”, suna masu nuni ga harin baya-bayan nan a Bamako da harin 2023 a garin Djibo.

Kasashen na tuhumarsa da babban laifin hada baki wajen ayyukan ta’addanci da goyon bayan ‘yan ta’adda, in ji sanarwar.

Dama tun tuni hukomomin mulkin soji a kasashen uku suka dakatar da watsa shirye shirye na tashar France 24 dama wasu kafafen yada labarai faransa a kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments