Watsa da hankali na jaridar New York Times, kan cewa Iran ta yi barazanar kashe Trump

New York Times wacce kafar watsa labarai ce ta Amurka, ta matsa kaimi a baya bayan nan kan wani labarinta data kasa bada hujja akansa

New York Times wacce kafar watsa labarai ce ta Amurka, ta matsa kaimi a baya bayan nan kan wani labarinta data kasa bada hujja akansa na zargin iran da barazanar kasha tsohon shugaban Amurka D Trump, kana kuma dan takara a zaben shugabancin kasar na watan Nuwamba mai zuwa.

jaridar maimakon ta bayar da hujjoji na gaske ko bayanai masu gamsarwa, na dogaro ne kawai da hujjojin data tsunto nan da cen wadanda kuma karara na tsokana ne ko kuma karkata hankula game da zabukan kasar dake tafe.

A wata makala wacce Chris Cameron ya wallafa a ranar 24 ga Satumba, 2024, jaridar New York Times ta kawo bayani game da barazanar kisa na Iran”kan tsohon shugaba Trump, tare kuma da ruwaito zargin ofoshin yakin neman zaben Trump na cewa Iran ta yi barazanar kashe Donald Trump,

Wannan karara irin wannan rahoto a fili ya nuna kokarin da ake yi na amfani da sunan Iran a matsayin wata barazana ta haifar da cece-kuce a zaben.

A cikin wannan labarin, an yi iƙirari game da barazanar kashe Donald Trump da Iran ta yi, amma ba a bayar da takamammen shaida ko hujjoji game da waɗannan ikirari ba. Ire-iren wadannan labaran, ban da kokarin janyo hankalin jama’a a duniya, da alama an tsara su ne a siyasance don jan hankalin jama’a a daidai lokacin da zaben Amurka ke gabatowa.

An tsara rahoton ne a matsayin wani bangare mai girman gaske kuma mai hatsarin da zai yiwa Amurka barazana, ba tare da bayar da cikakkun bayanai ko gamsassun hujjoji da ke tabbatar da wadannan zarge-zarge ba, Musamman ma, rashin tabbas da ke tsakanin waɗannan barazanar da ake zargi da kuma wasu abubuwan da suka shafi tsaron Trump,

Wannan nau’in watsa labarai na iya zama wani ɓangare na dabarun siyasa da kuma karkatar da hankali daga batutuwa na ainihi kamar kudaden harajin Amurka da ake amfani dasu wajen samar da makamai ga Ukraine da Isra’ila, ko don ɓoye raunin cikin gida na Amurka.

Daga cikin sukar har da tuhume-tuhume da ake yi wa Iran kan satar bayanai da yada labaran karya, ba tare da kwakkwarar hujja ba.

A ƙarshe, waɗannan rahotannin ba su taimakawa tsaro ko manufofin Amurka, sai dai kawai suna taimakawa wajen lalata amincin kafofin watsa labarai na kasar da kuma raunana ɗabi’ar al’ummar Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments