Pezeshkian Ya Karyata Da’awar Amurka Na Cewa Iran Na Da Shirin Kera Makamin Nukiliya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta bukatar kera makamin nukiliya kamar yadda Amurka take ikirari Shugaban kasar Iran Masoud

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta bukatar kera makamin nukiliya kamar yadda Amurka take ikirari

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta neman kera wani makamin nukiliya, kuma gwamnatin Amurka ta yi karya game da wannan batu.

Shugaba Pezeshkian ya fada a wata hira da yayi da tashar talabijin na CNN a birnin New York cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta bukatar mallakar makamin nukiliya ba, kuma Amurka karya take yi cewa Iran tana da boyayyen Shirin neman mallakar makamin nukiliya da kuma yada bayanai marasa tushe da rashin dacewa kan Iran game da         Iran ga duniya.

Shugabn ya kara da cewa: Iran ta amince da shirin aiwatar da aikin hadin gwiwa, kuma tana aiwatar da duk yarjejeniyar da ta da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta IAEA karkashin mafi girman matakin sa ido kan ayyukan nukiliyarta cikin lumana.

Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Iran tana kera makamai masu linzami, domin neman kare kanta ne kawai, yana mai nuni da cewa: A lokacin yakin da Saddam Hussein ya kakaba wa Iran tare da taimakon Amurka da wasu kasashen Turai, ya yi luguden wuta kan Iran da makamai masu linzami har muggan makamai da ya samu daga kasashen Turai da Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments