Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Kan Yankunan Kasarta

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani ga zargin Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa dangane da tsibiran Iran guda uku Kakakin ma’aikatar harkokin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani ga zargin Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa dangane da tsibiran Iran guda uku

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya yi Allah wadai da sanarwar hadin gwiwa da shugabannin Amurka da na Hadaddiyar Daular Larabawa suka fitar dangane da tsibiran Iran guda uku, Tumb Babban da Tumb Karami da kuma Abu-Musa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba ya jaddada cewa: Tsibiran Iran guda uku Tumb Babban da Tumb Karamar da Abu-Musa, wasu bangarori ne na yankin kasar Iran da ba za a iya raba su da Iran ba, don haka duk wani bayani da wasu bangarori suka fitar game da su gaba daya ba shi da tushe ballantana makama.

Kan’ani ya ci gaba da cewa: Maimaita zarge-zarge marasa tushe da Hadaddiyar Daular Larabawa ke yi kan tsibiran Iran guda uku, da fitar da bayanan siyasa na hadin gwiwa daga wannan kasa da sauran bangarori da sukekawance da ita, ba su da wani tushe, kuma ba za su haifar da cikas ga yanayin shari’a da ke kan wadannan tsibiran na Iran guda uku ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments