Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan ya isa birninNew York domin halartar zaman babban taron zauren Majalisar
Shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a Sudan kuma babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Abdul-Fattah Al-Burhan ya isa birnin New York na kasar Amurka a karkashin jagorancin tawagar kasar Sudan dake halartar zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79, kuma zai gabatar da jawabin Sudan a yau Alhamis 26 ga watan Satumba.
Ministan harkokin wajen Sudan ya bayyana cewa; Jawabin na Al-Burhan zai fi mayar da hankali ne kan batun cikin gidan Sudan da yakin da aka dorawa kasar, sannan zai yi jawabi ga kasashen duniya da su dauki Sudan a matsayin kasa mai cin gashin kanta, ba wai fassara abin da ke faruwa a matsayin yakin cikin gida ba. amma a maimakon haka yaki ne na waje da kasashen yankin ke taka rawa a ciki a bangarori daban-daban.
Ministan harkokin wajen Sudan ya bayyana cewa: Sun tattauna da takwarorinsa na wasu kasashe musamman kan batutuwan sake gina kasar Sudan bayan kawo karshen yakin da aka dora wa kasar.