Hukumar “Unrwa” Ta Yi Gargadi Akan Yiyiwar Mayar Da Lebanon Daidai Da Gaza

Shugaban hukumar Agaji ta “Unrwa” Phillip Lazarini ya bayyana cewa;  yankunan Gaza da yammacin Kogin Jordan sun zama fagen daga, a halin yanzu kuma kasar

Shugaban hukumar Agaji ta “Unrwa” Phillip Lazarini ya bayyana cewa;  yankunan Gaza da yammacin Kogin Jordan sun zama fagen daga, a halin yanzu kuma kasar Lebanon ta bi sahu da hakan yake nufin jefa mutanen yankin cikin matsala.

Shugaban hukumar Agajin ta Falasdinu ya ce, idan har cikakken yaki ya barke a Lebanon to yanayin kasar zai yi kama da na Gaza.

A gefe daya, ministan harkokin wajen Lebanon Abdullah Bu Habib ya ce, ya zuwa yanzu adadin ‘yan hijirar Lebanon ya kai rabin miliyan.

A ranar Litinin da safe ne dai HKI ta far kai wa kudancin Lebanon hare-hare masu tsanani, da har yanzu yake cigaba.

Ita kuwa ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ya sanar da cewa,adadin wadanda su ka yi shahada ya kai 570, dfaga cikinsu da akwai kananan yara 50, da kuma mata 94. Rahoton ya kuma bayyana cewa, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 850.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments