Akalla Mutane 558 Ne Suka Yi Shahada A Kasar Lebanon, 50 Daga Cikinsu Yara, Saboda Hare Haren HKI

Yawan wadanda suka rasa rayukansu ko shahidai a kasar Lebanon sanadiyyar hare haren jiragen yakin HKI kan kasar a yanzun ya kai 558, kuma akwai

Yawan wadanda suka rasa rayukansu ko shahidai a kasar Lebanon sanadiyyar hare haren jiragen yakin HKI kan kasar a yanzun ya kai 558, kuma akwai yiyuwar wannan adadin ya karu saboda har yanzun Jami’an kwana-kwana da kuma masu sa kai suna ci gaba da zakulo wasu karin gawaki a wasu gine-ginen wadanda suka rushe.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, kasashen duniya sun ci gaba da yin allawadai da HKI dangane da wadannan hare hare, musamman kan fararen hula da sunan mayakan kungiyar Hizbullah suna boye a tsakaninsu.

Yawan wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar yake yake da HKI take yi a Lebanon dai ya kai adadin mafi yawa idan an kwatanta da yake yaken HKI da Hizbullah shekaru 35 da suka gabata.

A wani labarin kuma kakakin fadar Krimlin na kasar Rasha Dmitry Peskov ya ce yakin da aka fara a kasar Lebanon ya na da hatsari, saboda yana iya yaduwa zuwa dukkan kasashen kudancin Asiya.

Haka kuma mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mariya Zakharova ta yi kira da a kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar Lebanon da Gaza saboda ya na da hatsari, don ya na iya fita daga yanayinda za’a iya kawo karshensa.

Sai kuma kasar China, wacce ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi,  ya fadawa tokwaransa na kasar Lebanon kan cewa kasar China tana goyon bayan kasar Lebanon sannan ya   bayyana cewa jiragen yakin HKI suna kashe fararen hula da kuma mata da yara ne a hare haren da take kaiwa kan gidajen mutane a kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments