Pezeshkiyan: Bai Kamata Duniya Ta Zuba Ido Tana Ganin HKI Ta Maida Lebanon Wani Gaza Ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa yakin da ke faruwa a Gaza ya kara fadada zuwa kasar Lebanon, don haka ba zamu bar

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa yakin da ke faruwa a Gaza ya kara fadada zuwa kasar Lebanon, don haka ba zamu bar HKI ta maida kasar Lebanon wani gaza ba.

Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadar haka ne a hirar da ta hada shi da dan rahoton tashar talabijin ta CNN a birnin New York Fareed Zakaria a yau Talata.

Shugaban ya kara da cewa bai kamata kasashen duniya su zuba ido suna ganin HKI ta maida kasar Lebanon wata gaza ba bayan yaki tsakaninsu na karshe a shekara ta 2006.

Shugaban  ya kara da cewa HKI tana samun tallafi daga kasashen Turai da kuma Amurka, wadanda suke da makamai mafi muni a duniya, sai dai duk da haka nasara tana ga wadanda aka zalunta.

Ya kuma kammala da c ewa akwai yiyuwar wannan yakin ya kara fadada zuwa kasashen yankin kuma a dade ana fafatawa.

Shugaban Pezeshkiyan dai yana birnin NewYork na kasar Amurka ne don halattan taron babban zaurenMDD karo na 79.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments