Mai Magana Da Yawun Gwamnatin Iran Ta Bayyana Cewa Gwamnatin Kasar Tana Son Bunkasa Amfani Da Makamashi Wanda Baya Bata Yanayi

Maimagana da yawan gwamnatin kasar Iran Fatimah Mohajerani ta bayyana cewa gwamnatin shugaba Pezeshkiyan tana da Shirin samar da makamashi mai tsabata a kasar saboda

Maimagana da yawan gwamnatin kasar Iran Fatimah Mohajerani ta bayyana cewa gwamnatin shugaba Pezeshkiyan tana da Shirin samar da makamashi mai tsabata a kasar saboda samar da yannayi mai tsabta a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Mohajerani tana fadar haka a jawabinta na farko da yan jarida, tun bayan nadata a matsayin mai magana da yawun gwamnatin shugaba Pezeshkiyan.

Fatimah ta kara da cewa amfani da makamashi mai tsabta ya na daga cikin Shiri na 7Th na cigaba wanda majalisar dokokin kasar ta maida shi doka. Kuma aikin gwamnatin ne ta aiwatar da dokokin da majalisar dokoki ta kafa.

Shirin ci gaban kas ana 7th ya bukaci a samar da karin megawats 2,000 na wutan lantarki tare da amfanida makamashin nukliya.

Don haka ana saran kafin karshen Shirin na ci gaba kashi na 7th wanda ake bukatar a aiwatar da shi a cikin shekaru 5 masu zuwa, wato daga watan Maris na wannan shekara ta 2024 zuwa watan Maris na shekara ta 2030 gwamnatin kasar Iran zata aiwatar da Shirin.

Mai Magana da yawun gwamnatin Iran ta kara da cewa Shirin ci gaban kasa na 7th dai yana da bangarori 22, 7 daga cikinsu sun shafi ci gaba a banagren tattalin arziki, manya manyan ayyuka, zamantakewa da al-adu, ilmin kimiya, da kere-kere da tarbiyya, da harkokin waje da tsaro da kariya,  gudanarwa da kuma sharia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments