Pezeshkian: Makircin Isra’ila na fadada yaki ba zai amfanar da kowa ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce; Isra’ila na hankoron ganin ta jefa daukacin yankin a cikin wani mummunan yaki da rashin tsaro, wanda ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce; Isra’ila na hankoron ganin ta jefa daukacin yankin a cikin wani mummunan yaki da rashin tsaro, wanda ba zai amfani wata kasa ba.

Pezeshkian wanda yanzu haka yake birnin New York domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan kafafen yada labaran Amurka a wannan Litinin.

Pezeshkian ya ce Iran tana kare al’ummar Palastinu da ake zalunta. Shugaban na Iran ya soki yadda manyan kafafen yada labarai na duniya suka kasa daukar mataki kan yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza.

Da yake amsa tambaya game da karfin tsaron Iran, Pezeshkian ya ce Tehran ba ta neman kaddamar da yaki da yada rashin tsaro, kuma ba ta taba kaddamar da wani hari a kan wata kasa ba.

Da aka tambaye shi game da martanin da Iran ta mayar kan kisan da Isra’ila ta yi wa Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas a Tehran a karshen watan Yuli, Pezeshkian ya ce wannan mummunan aiki wanda aka yi Allah wadai da shi bisa dukkan dokokin kasa da kasa, ba zai wuce ba tare da mayar da martani ba.

Ya kara da cewa Iran ta tabbatar da cewa tana iya maida martani mai karfi kan laifukan Isra’ila, duk da cewa kasar ba ta neman yada rashin zaman lafiya da rashin tsaro a yankin.

An kashe Haniyeh ne a ranar 31 ga watan Yuli a lokacin da yake birnin Tehran domin halartar bikin rantsar da shugaba Pezeshkian.

Jagorancin siyasa da na soja na Iran ciki har da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, sun sha alwashin daukar fansa kan jinin Haniyyah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments