Shugaban Iran Ya Jadadda Aniyar Kasarsa Na Daukan Fansar Kisan Isma’il Haniyyah

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Kisan gillar shahidi Isma’il Haniyyah ba zai shige ba tare da daukan fansa ba Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Kisan gillar shahidi Isma’il Haniyyah ba zai shige ba tare da daukan fansa ba

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce a duniyar da ake kashe fararen hula a Zirin Gaza da kuma goyon bayan kisan kiyashi da ta’addanci, ba za a taba samu kwarin gwiwar tabbacin zaman lafiya ba.

A yayin jawabinsa a gaban babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Kakaba takunkumin bangaren guda yana kawo cikas ga cimma nasarar ci gaba mai dorewa, yana kiran da a gaggauta gudanar da gyare-gyare a tsarin da ke                                jagorantar duniya da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, domin shigar da kasashe masu tasowa cikin shawarwarin duniya.

Pezeshkian ya kara da cewa: Fuskantar kalubale a halin yanzu da abin da zai zo nan gaba suna bukatar hadin kai da taimakekkeniya da suka kafu a kan tubalin adalci da gaskiya, yana mai jaddada wajabcin daukan matakin raba duniya da makaman nukiliya ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Shugaban ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta mayar da martani kan harin wuce gona da iri da aka kai kan karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus na kasar Siriya, wanda da tabbatar da cewa tana da karfin mayar da martani kan laifukan wannan haramtacciyar kasa ‘yar mamaya.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kisan gillar da aka yi wa shahidi Isma’il Haniyeh abin yin Allah wadai ne a dukkan dokokin kasa da kasa, kuma ya jaddada cewa; Babu shakka ba zai shige ba tare da mayar da martani ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments