Somaliya ta zargi makwabciyarta Habasha da samar da makamai ga yankinta na Puntland dake arewa maso gabashin kasar, wanda a bana ya bayyana cewa zai shelanta zama kasa mai cin gashin kanta duk da rashin amincewar da gwamnatin Somalia ta nuna kan hakan.
Akwai tarihin dangantakar da ke tsakanin Habasha da Somaliya da kuma wannan yanki mai wanda rashin zaman lafiyarsa ya raunana karfin gwamnatin tsakiyar kasar na tinkarar matsalar tada kayar baya na kungiyar al-Shabaab.
Rikici tsakanin kasashen yankin kahon Afirka ya kara ta’azzara ne tun daga farko watan Janairun wannan shekara, lokacin da Addis Ababa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da yankin arewacin Somaliya, Somaliland, yankin da ya sanar da ballewa daga kasar, wanda ya bai wa Habashadamar da ta dade tana nema domin kaiwa ga teku.
“Somaliya ta yi Allah wadai da jigilar makamai ba tare da izini ba daga Habasha zuwa yankin Puntland na Somalia, da keta ikon kasar da kuma yin barazana ga tsaron yankin,” in ji ma’aikatar harkokin waje a Mogadishu.
Somaliland tana tsakanin iyakar Habasha da Puntland.