Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada A El-Fasher Na Sudan, Yayin Kwalara Ke Lashe Rayukan Mutane A Kasar

A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a birnin El Fasher tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa, cutar kwalara

A daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a birnin El Fasher tsakanin sojojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa, cutar kwalara tana ci gaba da lashe rayukan daruruwan jama’a a kasar

Rahotonni suna bayyana cewa: An sake samun bullar kazamin fada da lugudan bama-bamai tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa a birnin El-Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa, yayin da adadin wadanda suka mutu sakamakon bullar annobar kwalara ya kai mutane 348 a kasar tun daga watan Agustan da ya gabata.

Majiyoyin yada labarai sun ruwaito cewa: Tun daga ranar Alhamis ake ta gwabza kazamin fada a birnin El Fasher, sakamakon hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa suka kai kan birnin da nufin kwace iko da shi.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa: Jiragen saman yakin sojojin Sudan sun kaddamar da hare-hare ta sama a kan wuraren da dakarun kai dauki gaggawa na Rapid Support Forces suke a arewa da gabashin kudancin birnin El Fasher.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments