Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sake Kera Wani Makami Mai Linzami Mai Dauke Da Ci Gaba Matuka

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna wani sabon makami mai linzami da ta kera a karon farko A yayin faretin soji na sojojin Iran a

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna wani sabon makami mai linzami da ta kera a karon farko

A yayin faretin soji na sojojin Iran a yau Asabar, an baje kolin sabbin makamai masu linzami masu cin dogon zango da wasu sabbin makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka kera mai suna “Jihad”.

A yayin faretin soji na Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) an baje kolin makamai masu linzami nau’i guda 21 da suka hada da makami mai linzami na “Jihad” a karon farko, baya ga makamai masu linzami na “Khyber Khan” guda biyu, makami mai linzami na “Fatah” guda 4, da makami mai linzami na “Haj Qassem” guda 4, da makami mai linzami na “Qadr H”, da makami mai linzami na “Imad” guda 2, da makami mai linzami na “Khorramshahr” guda 3, da kuma makami mai linzami na “Sejil” guda 4.

Makami mai linzami na “Jihad” shi ne makami mai linzami na baya-bayan nan na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na sojojin sama suka kera.

Makami mai linzami mai suna “Jihad” wani sabon nau’in makami ne da    ke cin dogon zango na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, wanda ke da tsari da ci gaban zamani na musamman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments