Iran Da Burkina Faso Sun Rattaba Hannu Kan Hadin Gwiwa a Fannin Sarrafa Makamashin Nukiliya

An cimma yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin sarrafa makamashin nukiliya tsakanin Iran da Burkina Faso Kasashen Iran da Burkina Faso sun rattaba hannu kan wata

An cimma yarjejeniyar hadin gwiwa a fannin sarrafa makamashin nukiliya tsakanin Iran da Burkina Faso

Kasashen Iran da Burkina Faso sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa, inda mataimakin shugaban kasar kuma shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ya rattaba hannu a bangaren Iran, sannan ministan kimiyya da ilimi mai zurfi a bangaren Burkina Faso ya rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar.

An rattaba hannu ne kan yarjejeniyar fahimtar juna kan ayyukan masana’antar nukiliya cikin lumana a gefen taron shekara shekara na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a Vienna.

A ziyarar da ya kai birnin Vienna domin halartar babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya karo na 68, mataimakin shugaban kasar kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran Muhammad Islami, ya gana da ministan kimiyya da Ilimi mai zurfi na kasar Burkina Faso, inda suka yi musayar ra’ayoyi kan hanyar bunkasa alaka tsakanin kasashen ta bangarori da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments