Iran Ta Kira Jakadan Afganistan A Tehran Saboda Bayyana Korafinta Na Rashin Mutunta Taken Kasar

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bukaci jakadan kasar Afganistan a Tehran ya zo ma’aikatar, don isar masa da sakon korafinta saboda rashin mutunta taken

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bukaci jakadan kasar Afganistan a Tehran ya zo ma’aikatar, don isar masa da sakon korafinta saboda rashin mutunta taken kasar wanda wakilin kasar Afganistan a taron hadin kan musulmi karo na 38 a nan Tehran ya yi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto labarin na cewa a jiya Alhamis ne aka bude taron hadin kan kasashen musulmi wanda ake kira makon hadin kai karo 38th .

Labarin ya kara da cewa wakilin kasar Afganistan a taron ya ki tashi tsaye a lokacinda ake rare taken kasar Iran a lokacin bude taron.

Jakadan kasar Afganistan a Tehran ya amsa gayyatar ya kuma saurari korafin JMI, sannan ya ce zai isar da sako zuwa ga gwamnatin kasarsa da gaggawa. Banda haka jakadan ya kara da cewa wakilin kasar Afganistan a taron na hadin kan al-ummar musulmi yayi haka ne a karan kansa ba yana wakiltan gwamnatin kasar Afganistan ba ne.

Jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran daga karshe ya ce wannan halin da wakilin kasar Afganistan ya nuna ya sabawa manufar zuwansa taron kwatakwata. Don tarona na hadin kai da mutunta juna ne a tsakanin musulmi.

Labarin ya kamala da cewa a yau Jumma’a, wikilin kasar Afganistan a taron na hadin kan kasashen musulmi ya yi wani sako bidiyo don bawa JMI hakuri kan abinda ya faru. Sannan ya ce bai ki tashi a lokacin da ake rare taken JMI don cutar da wani ba.

Malaman addinin musulunci daga mazhabobin shia da sunnan kimani 144 ne suke halattan taron na hadin kan musulmi a nan Tehran daga kasashe 36.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments