Jakadan kasar Lebanon a MDD ya bayyana cewa na’urorin sadarwan da HKI ta tarwatsasu a hannun mutanen kasar lebanon, bincike ya tabbatar da cewa an rika an sanya nakiyoyi masu fashewa a cikin su kafin su shigo kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a ranakun Talata da laraban da suka gabata ne, na’urorin sadarwa na ‘Pager’ da waki-toky fiye da 3000 ne suka farfashi a hannun masu amfani da su a duk fadin kasar da kasar Siriya.
Labarin ya kara da cewa mutane 37 suka rasa rayukansu a duk fadin kasar sanadiyyar tashin nakiyoyin da suke cikinsu. Sannan wasu kimani 3000 suka ji raunuka. Gwamnatin HKI ta tabbatar da cewa ita ce ta tada boma bomai a cikin na’urorin sadarwan, kuma tana nufin halaka mayakan Hizbullah wadanda suke amfani da su ne.
Labarin ya kara da cewa kamfanonin da suka shigo da na’urorin cikin kasar sun sanya nikoyoyin sannan sun tadasu ta hanyar aika sakon e-mail zuwa cikinsu.
Masana suna ganin hare hare kan na’urorin sadarwan da HKI ta kai wa mutanen Lebanon zai shafi kokarin da ake na tsagaita wuta a yakin da HKI take fafatawa da kungiyar Hizbullah.
Banda haka a yau Jumma’a ce ake saran kwamitin tsaro na MDD zai gudanar da taron gaggawa don tattauna batun hare haren na HKI.