Aljeriya ta kirayi zaman gaggawa na kwamitin sulhu kan abubuwan dake faruwa a Lebanon

Aljeriya ta yi kira, bisa bukatar Lebanon, da a gudanar da wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhu, don yin nazari kan abubuwan da ke faruwa

Aljeriya ta yi kira, bisa bukatar Lebanon, da a gudanar da wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhu, don yin nazari kan abubuwan da ke faruwa masu hadari a Lebanon, musamman ma babban harin fashewar na’urorin sadarwa.

Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ahmed Ataf ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Labanon Abdallah Bou Habib, wanda ya jajantawa Lebanon kan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin da Isra’ila ta kai kan kasar.

A yayin zantawar, Ataf ya bayyana cewa, gaba daya kasar Aljeriya tana goyon bayan kasar Lebanon, da kuma tsayawa tsayin daka bisa la’akari da mawuyacin halin da take ciki, sakamakon ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa  da ke yin barazana ga tsaro da zaman lafiya na kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments