Sanata Sanders ya gabatar wa Majalisa wata doka da ta dace ta dakatar da sayar wa Isra’ila makamai

Sanatan Amurka Bernie Sanders ya tabbatar da cewa kashi 60% na wadandfa suka rasa rayyukansu a yakin da Isra’ila ke kaddamarwa kan Gaza mata ne

Sanatan Amurka Bernie Sanders ya tabbatar da cewa kashi 60% na wadandfa suka rasa rayyukansu a yakin da Isra’ila ke kaddamarwa kan Gaza mata ne da kananan yara, yana mai cewa kashi 90% na mazauna Gaza suna gudun hijira saboda yakin.

Sanata Bernie Sanders na Amurka ya tabbatar da cewa “akwai karin kisan kiyashi a Gaza, wanda ake yi da kayan aikin soja na Amurka”, ya kuma yi tambaya: “Me ya sa Amurka ta amince ta sayar da wasu makamai na dala biliyan 20 ga Isra’ila?”

Ya kuma ce zai matsa lamba”domin haramta wadannan makamai. Yakin Netanyahu ba shi da iyaka”. In ji Sanders.

Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta bayar da wani rahoto a  ‘yan makonnin da suka gabata, kan matakin da gwamnatin Burtaniya ta dauka na dakatar da wasu makamai da take fitarwa zuwa “Isra’ila” ba tare da bata lokaci ba, sakamakon keta dokokin jin kai na kasa da kasa.

Jaridar ta ambaci sanarwar da Italiya ta bayar a karshen shekarar da ta gabata cewa ta daina aika makamai zuwa Isra’ila, saboda mutunta sharuddan haramta yin amfani da makamai kan fararen hula.

A Netherlands, kotu ta umarci gwamnati da ta dakatar da fitar da sassan jirgin yaki na F-35 zuwa Isra’ila, saboda a fili hadarin da ke tattare da hakan ya  keta dokokin jin kai na kasa da kasa.

Dangane da kasar Beljiyam, kafofin yada labaran kasar sun rawaito cewa, yankin Wallonia ya dakatar da fitar da foda zuwa Isra’ila a cikin watan Fabrairun da ya gabata, biyo bayan bayar da umarnin da kotun kasa da kasa ta yi, inda ta umurci Isra’ila da ta kara kaimi wajen hana kisan fararen hula a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments