Amurka ta ce tana kokarin amfani da diflomasiyya domin kauce wa ta’azzarar tashin hankali tsakanin kungiyar Hezbollah da Isra’ila.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro, John Kirby ya jaddada kokarin Amurka na yayyafa wa wutar ruwa.
Ya kara da cewa abun da Amurka ke yi shi ne kauce wa tashin hankalin, duk da lamarin ba mai sauki ba ne amma mun yi amanna za a iya shawo kan matsalar.
Shi ma Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a cikin wani faifan bidiyo, ya tabbatar da cewa “hanyar diflomasiya ce kawai mafita a wanzu. »
Shugabannin diflomasiyyar Faransa da na Amurka sun yi kira daga birnin Paris ga dukkan bangarorin da su kaucewa jefa yankin cikin yaki.
Suna masu cewa “sun damu matuka” saboda hare-haren da ake kaiwa kungiyar Hizbullah a kasar Labanon.