Iran Ta Goyi Bayan Kudurin Babban Zauren MDD Na Neman A Kawo Karshen Mamayar Falasdinu Da Kuma Tsarin Wariya

JMI tana daga cikin kasashen wadanda suka amince da kawo karshen mamayar da gwamnatin HKI take wa kasar Falasdinu, da kuma kawo karshen tsarin mulkin

JMI tana daga cikin kasashen wadanda suka amince da kawo karshen mamayar da gwamnatin HKI take wa kasar Falasdinu, da kuma kawo karshen tsarin mulkin wariya a kasar a zaben da aka gudanar a babban zauren MDD a jiya Laraba.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, a jiya Laraba ce babban zauren MDD ya bukaci gwamnatin HKI ta kawo karshen mamayar da take wa kasar Falasdinu a cikin watanni 12 masu zuwa.

Kasashe 124 ne suka amince da kudurin da aka gabatar don wannan bukatar a yayinda kasashe 43 suka ki kada kuri’unsu, amma kasashe 14 daga cikin har da Amurka da kuma HKI suka ki amincewa da kudurin.

JKI ta bukaci kasashen duniya su tilastawa HKI ta amincewa dukkan Falasdinawa wadanda aka kora daga kasarsu su koma gida sannan ta mayar masu dukiyoyinsu da gidajensu da ta kwace ko ta lalatasu.

Har’ila ta yi kira ga kasashen duniya su dakatar da aika kayakin gine gine masu shiga HKI su bar sayar mata su, sannan su kawo karshen bata makamai da kuma kayakin soje wadanda take kashe falasdinawa da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments