Hezbollah: Isra’ila Za Ta Fuskanci Sakamakon Ayyukan Ta’addancinta a Lebanon

A cikin wani bayani da Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar, ta jaddada cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan  haramtacciyar kasar

A cikin wani bayani da Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar, ta jaddada cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan  haramtacciyar kasar Isra’ila domin nuna goyon bayanta ga al’ummar zirin Gaza da ke fama da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a kansu.

Haka nan kuma kungiyar ta ce, danyen aikin da Isra’ila ta yi a baya-bayan nan da ya yi sanadin salwantar rayukan al’ummar kasar Labanon zai kara karfafa azamar ci gaba da bin tafarkin gwagwarmaya da tsayin daka a gaban zaluncin masu girman kai.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan wasu munanan fashe-fashe da aka samu  a lokaci guda a fadin kasar Lebanon a wannan Talata.

Sannan kuma rahotanni sun bayyana cewa, na’urorin da aka dasa a cikin na’urorin sadarwa wadanda aka fi sani da pagers, sun tarwatse a wurare daban-daban. A cikin Labanon da Syria

A nasa bangaren ministan lafiya na kasar Lebanon Firass Abiad ya ce akalla mutane goma sha biyu ne suka hada da kananan yara biyu ne suka rasa rayukansu a wannan harin ta’addanci na Isra’ila.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a wannan Larabar, inda ya ce kimanin wasu 3,000 ne kuma suka jikkata a harin. Wadanda suka jikkata sun hada da ‘yan gwagwarmaya da kuma fararen hula.

Tun da farko dai, Hezbollah ta ce bayan ta nazarci duk wasu bayanai da kuma bayanan da ake da su game da hare-haren, ta dora alhakin hakan a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kungiyar ta kuma kara da cewa a cikin sanarwar da ta fitar, tsarin gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon zai ci gaba kamar yadda yake, kuma babu gudu babu ja da baya wajen ci gaba da taimakon al’ummar Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments