Hizbollah Ta Lashi Takobin Ci Gaba Da Kai Hare-haren Goyan Bayan Falasdinu  

Kungiyar Hizbullah ta lashi takobin ci gaba da kai hare-haren kin jinin haramtacciyar kasar Isra’ila domin nuna goyon baya ga al’ummar Gaza da ke fama

Kungiyar Hizbullah ta lashi takobin ci gaba da kai hare-haren kin jinin haramtacciyar kasar Isra’ila domin nuna goyon baya ga al’ummar Gaza da ke fama da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi, inda ta bayyana cewa hare-haren baya-bayan nan ta hnayar karamar na’uarar sadarwa da Isra’ila ta kai wanda ya yi sanadin salwantar rayuka a Labanon zasu kara karfafa gwagwarmaya da tsayin daka.

Sanarwar ta Hezbollah ta zo ne bayan wasu munanan fashe-fashen da aka yi a lokaci guda a fadin kasar Lebanon a ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa, na’urorin da aka dasa a cikin kananan na’urorin sadarwa, wadanda aka fi sani da pagers, sun tarwatse a wurare daban-daban.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta ce akalla mutane tara ne suka mutu yayin da wasu 2,800 suka samu raunuka sakamakon fashe-fashen.

Wadanda suka jikkata sun hada da ‘yan gwagwarmaya da kuma fararen hula.

Yau Laraba kungiyar Hizbullah ta sanar da shahadar mayakanta 12, saidai ba ta bayyana ko an kashe su ba a fashe-fashen ko kuma harin da aka kai a wasu wurare.

Tun da farko dai, Hezbollah ta ce bayan ta nazarci duk wasu bayanai da kuma bayanan da ake da su game da hare-haren, ta dora alhakin hakan ga gwamnatin Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments