Majalisar Dinkin Duniya na kada kuri’ar neman kawo karshen mamayar Isra’ila

A wani lokaci yau ne Majlisar Dinkin Duniya, za ta kada kuri’ar neman kawo karshen mamayar da Isra’ila ke wa falasdinu. Wannan dai na zuwa

A wani lokaci yau ne Majlisar Dinkin Duniya, za ta kada kuri’ar neman kawo karshen mamayar da Isra’ila ke wa falasdinu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran sama da shugabannin duniya 180 za su halarci babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda ake sa ran yakin Gaza zai mamaye tattaunawar ta bana.

Tawagar Falasdinawa ta yi kira ga kasashe da su bukaci kawo karshen mamayar da Isra’ila ke yi a yankunanta yau kusan watanni 12.

Wannan shi ne karo na farko da ta gabatar da wani daftari da kanta, kuma ta yanke shawarar dogaro da shawarwarin kotun duniya da ta yi la’akari da cewa ci gaba da kasancewar Isra’ila a yankin Falasdinawa da ta mamaye tun shekara ta 1967 haramun ne.

Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, bai bata lokaci ba, inda ya yi aiki tare da wasu kasashen Larabawa wajen tsara kudurinsa na farko.

A watan Yulin da ya gabata ne dai kotun ta ICJ da ta yi nazari kan mamayar Isra’ila tun daga shekarar 1967 bisa bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta gano cewa “ci gaba da kasancewar Isra’ila a yankin Falasdinawa da ta mamaye haramun ne”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments