Fizishkiyan: Za Mu Kare Hakkokin Al’ummar Iran A Taron MDD

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa, Iran ba kasa ce ‘yar ina da yaki ba, kuma idan ya halarci taron MDD zai kare

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa, Iran ba kasa ce ‘yar ina da yaki ba, kuma idan ya halarci taron MDD zai kare hakkokin al’ummar Iran.

Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa, zai halarci taron MDD wanda za a yi a birnin Newyork a wannan makon, domin ya kare hakkokin al’ummar Iran.

A jiya talata ne dai shugaban na kasar Iran da ya gabatar da jawabi a gaban majalisar shawarar musulunci ta kasar bayyana hakan, yana mai kara da cewa, a cikin shekaru 200 da su ka gabata, Iran ba ta yaki wata kasa ba, ko sau daya,amma abokan gaba ne su ke yin abin bai dace ba.

Shugaban kasar na Iran ya kuma ce, makiya ne su ka damfara mana dukkanin matsalolin da muke fuskanta, su ka kuma kirkiri HKI a cikin wannan yankin, sannan su ka ba ta muggan makamai, sannan suke fada mana cewa kar mu mallaki makai, domin su bai wa ‘yan sahayoniya damar kai mana hari a duk lokacin da su ka ga dama.

Har ila yau shugaban na kasar Iran ya ce, Iran ba za ta taba rusunawa ba a gaban duk wanda yake son ya yi mu’amala da ita da girman kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments