Sinwar ga Sayyed al-Houthi: Mun tsaya tare a fagen kare karamar  al’umma

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya tabbatar da cewa gwagwarmaya a Zirin Gaza da kuma kungiyar Ansar Allah a kasar Yaman

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya tabbatar da cewa gwagwarmaya a Zirin Gaza da kuma kungiyar Ansar Allah a kasar Yaman suna yakar zaluncin Isra’ila kafada da kafada.

A cikin wani sako da ya aike wa jagoran kungiyar Ansar Allah, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, Sinwar ya ce: “Na ji dadin rubuta muku wannan sako a ranar maulidin Manzon Allah (saww), a daidai lokacin da muke yaki a karkashin guguwar Aqsa hannu da hannu.

Har ila yau ya tabo batun yakin da kuma hare-haren na Yaman a kan birnin Tel Aviv, inda ya jaddada cewa, guguwar Al-Aqsa ta yi mummunar illa ga shirin  yahudawan sahyoniya a yankin baki daya.

Shugaban Hamas ya taya Sayyed al-Houthi murnar nasarar da sojojin Yaman suka samu, inda wani makaminsu mai linzami ya isa har tsakiyar yankunan da Isra’ila ta mamaye a cikin Falastinu, inda ya ketare dukkan mamakan kariya da yahudawa gami da abokansy suka girka.

Sinwar ya jaddada cewa, aikin na sojojin Yemen ya kara karfafa  karfin gwagwarmaya da tasirinta yankin.

Ya kuma bayyana harin na Yaman a matsayin matakin koli, yana mai cewa ya isar da sako ga yan mamaya, “Jaruman sojojin kasar Yemen sun yi fice wajen bunkasa karfin soji da zai ba su damar shiga cikin rundunoni masu tasiri a yankin,” in ji Sinwar, inda ya kara nuna irin rawar da al’ummar Yemen ke takawab a dukkanin fagagae wajen taimakon al’ummar Falastinu, da cewa hakan babban jihadi ne abun yabawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments