Wani mamba a majalisar gudanarwa ta kasar Yemen ya bayyana cewa kasashen Amurak da Burtaniya sun aikawa gwamnatin kasar sako wacce ta bukaci ta dakatar da yakin da take da su da kuma HKI, su kuma a nasu bangaren zasu amince da ita a matsayin halacciyar gwamnati a duniya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Muhammad Al-Bukhaiti yana fadar haka ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Yemen ta yi watsi da wannan bukatar.
Gwamnatin kasar Yemen dai ta shiga yakin da HKI don tallafawa falasdinawa wadanda gwamnatin HKI take wa kissan kiyashi a gaza tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023. Kuma ta bayyana cewa ba zata dakatar da yaki da HKI da kuma kasashen Amurka da Burtaniya sai an dakatar da kissan kiyashin da suke yi a gaza.