Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Tehran a shirye ta ke ta tattauna da kasashen Yammacin duniya, kuma Ya ce gwamnatinsa za ta yi shawarwari da kasashen kan batutuwan da ake ta cece-kuce akansu.
Ya bayyana hakan ne a wannan Litinin yayin da yake ganawarsa da manema labarai na cikin gida da na ketare na farko da ya yi tun bayan hawansa karagar mulki a karshen watan Agusta.
“Ba mu cikin rikici da kowa, za kuma mu fadada hulda da kasashen makwabta domin inganta tattalin arziki da kuma cimma dogon buri,” in ji shugaban na Iran, lokacin da yake amsa tambayoyin manema labaran.
Duk da haka, ya kara da cewa Amurka da farko na bukatar tabbatar da cewa a shirye ta ke don yin shawarwari, saidai ya ce ya lura ya zuwa yanzu Amurkawa sun “rufe dukkan hanyoyin ka iwa ga hakan..”
A daya bangaren Shugaban na Iran ya ce halartar taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 a New York zai kasance “domin kare hakkin mutanenmu ne saboda muna son zaman lafiya ba yaki ba.”
Da aka tambaye shi game da yiwuwar ganawarsa da shugaban Amurka, Pezeshkian ya ce dole ne Amurka ta tabbatar da cewa da gaske ta ke.
Haka zalika shugaba Pezeshkian ya yi watsi da ikirarin cewa Iran ta baiwa Yemen makamai masu linzami ko fasahar kera makaman.
Pezeshkian ya jaddada muhimmancin saukaka tafiye-tafiye a tsakanin kasashen musulmi, wanda a cewarsa, zai haifar da ra’ayi daya da kafa kasuwannin hadin gwiwa.
Hadin kai tsakanin musulmi zai taimaka wajen kare hakkinmu, in ji shugaban na Iran.
Dole ne musulmi su samar da hadin kai don fahimtar da gwamnatin Isra’ila cewa ba ta da hakkin kashe yara, mata da tsofaffi, in ji shugaban na Iran. “Idan muka hada hannu, Isra’ila ba za ta kuskura ta yi hakan ba.”