Amurka : Meta Ya haramtawa kafafen yada labaran Rasha shiga dandalinsa a duk duniya

Kamfanin Meta na Amurka, mamallakin Facebook, TikTok, Instagram da WhatsApp, ya sanar a wannan Litinin cewa ya haramtawa kafafen yada labaran kasar Rasha shiga dandalinsa

Kamfanin Meta na Amurka, mamallakin Facebook, TikTok, Instagram da WhatsApp, ya sanar a wannan Litinin cewa ya haramtawa kafafen yada labaran kasar Rasha shiga dandalinsa a duk fadin duniya, a wani mataki da ya ce na kaucewa duk wani kushe ne daga ketare”.

‘’Mun fadada matakin da muke dauka kan kafafen yada labarai na kasar Rasha,” in ji Meta, kamfanin na Amurka.

Wannan haramcin na zuwa ne bayan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kalubanci ayyukan kafofin yada labarai na Rasha RT, wanda ya ce sun canza zuwa “reshe” na leken asirin Rasha a duniya.

Kimanin kwanaki 10 da suka gabata ne hukumomin Amurka suka gabatar da wani batu na matakan da suka shafi kafafen yada labarai na Rasha musamman, wadanda suka hada da gurfanar da masu laifi da kuma takunkumi, don mayar da martani ga yunkurin yin katsalandan a zaben Amurka, wanda suka alakanta da Rasha.

A cikin sakon da ta aike ta kafar sadarwa ta Telegram, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta yi wani shagube, tana mai cewa ya kamata a samar da sabon mukami a Amurka na :’’ kwararre kan takunkumi akan Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments